Hotunan budurwa mai shekaru 28 da wata yarinya mai shekaru 17 ta kashe a Kano


A ranar Alhamis 19 ga watan Augusta ne wata Aisha Kabiru mai shekaru 17 ta sharbawa makwabciyar ta, Bahijja Abubakar mai shekaru 28 wuka wanda hakan ne yayi sanadiyyar rasa ranta. Jaridar legit ta wallafa.

LIB ta ruwaito yadda mummunan lamarin ya faru a Shekar Maidaki Quaters dake karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano.


Wacce ake zargin ta amsa laifinta inda tace sun samu wata hayaniya ne da mamaciyar hakan ya janyo barkewar dambe a tsakaninsu.

Bayan an sasanta su ne daga baya ta dauki wuka mai kaifin gaske ta lallaba ta sharbawa Bahijja a wuyanta wanda ya kaiga ajalinta daga nan ta boye.

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana yadda lamarin ya faru, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Kakakin hukumar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda da ya saki a ranar Asabar, 21 ga watan Augusta ya ce Aisha ta sharba wa Bahijja wuka a wuya ta baya, inda tabar ta cikin jini.

Kamar yadda takardar tazo:

A ranar 19/08/2021 da misalin karfe 11pm muka samu rahoton yadda wata ta sharbawa Bahijja Abubakar mai shekaru 28 wuka a wuyanta ta tsere ta bart a cikin jini duk a Shekar Maidaki Quarters dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, a cewarsa.

Bayan samun wannan rahoton ne kwamishinan ‘yan sanda, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da umarni, inda yace SP Mudassir Ibrahim, DPO na yankin Kumbotso ya kai dauki.

Bayan isar ‘yan sandan ne suke zarce Asibitin kwararru na Murtala Mohammed dake Kano inda aka kwanta da ita. Sai dai washe gari da safe ta amsa kiran mahaliccinta a asibitin.

An kama Aisha Kabiru, mai shekaru 17 ‘yan anguwarsu mamaciyar da misalin karfe 10 na safe a Zawaciki Quarters dake karamar hukumar Kumbotso a inda ta boye.

Bayan ta sha tambayoyi da tsananin bincike, ta amsa laifinta inda tace dambe ne ya barke tsakaninsu amma bayan an shiryasu ta koma ta sharba mata wuka a wuya wanda hakan ne ya zama ajalinta.

Kwamishinan ‘yan sandan Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bayar da umarnin a mayar da lamarin ga bangaren binciken masu laifi na musamman don cigaba da zurfafa bincike. 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN