Hisbah a Kano ta kama Jaruma Sadiya Haruna ta kaita Kotu an yi mata hukunci, duba abin da ta yi


Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wata Jarumar Kannywood kuma ma'abuciyar amfani da shafukan sada zumunta, Sadiya Haruna  bisa zargin tura hotuna da bidiyon batsa a shafukan sada zumunta. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Sadiya wacce ke zaune a rukunin gidaje na Kabuga, ta fada hannun Hukumar Hisbah ne ranar Juma'a

Hisbah ta tsare ta har ranar Litinin 23 ga watan Agusta, daga bisani ta gurfanar da ita a gaban Kotun sharia da ke unguwar Sharada a birnin Kano.

Takardar kara da aka gabatar wa Kotu na tuhumar Sadiya, ta ce an gurfanar da ita ne a gaban Kotu bisa tuhumar yawan tura hotuna da bidiyon batsa, kuma tana rawa da bai dace ba a shafin Youtube, tare da yin kalaman batsa.

Rahotun ya ce wacce ake tuhuma a gaban Kotu ta amsa laifin aikata ba daidai ba, wanda ya saba wa sashe na 255 na dokar Penal Code 2000.

Bisa wannan dalili, Alkalin Kotun Ali Jibril Danzaki ya yanke mata hukuncin cewa ta dinga zuwa makarantar Islamiyya na Darul Hadith da ke unguwar Tudun Yola har tsawon wata shida.

Ya ce shugaban makarantar Islamiyyar da Hukumar Hisbah za su sa ido domin kula da da karatun da za ta yi a makarantar.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN