Hadaddiyar kungiyar agaji na jihar Kebbi sun saukar da Alqur'ani tare da fara addu'ar kwana 30, duba dalili


Hadaddiyar Kwamitin agajin Addinin Musulunci na jihar Kebbi, sun fara addu'a tare da saukar da Alqur'ani domin rokon Allah ya kawo mafita kan kalubalen tsaro da sauran masifu a jihar Kebbi da Najeriya gaba daya.

Kungiyoyin da suka hada da na JIBWIS, KTA, Annahdatul Islam, NAFSAT, JNI, CMS Central Mosque Birnin kebbi da sauransu, karkashin jagorancin shugabanta na jihar Kebbi Barrista Sanusi Danbuga, tare da sauran jigogi a kungiyar, sun kaddamar da fara adduar a garin Birnin kebbi ranar Lahadi  21 ga watan Agusta 2021 tare da sauje Alqur'ani nan take.

Sanusi Dan buga ya ce Kungiyoyin za su ci gaba da gudanar da addu'oin a kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar Kebbi har tsawon kwana 30.Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari