Yansanda sun kama wata mata bayan ta aikata wani mugun aiki a jihar Kano, duba abin da ta yiRundunar yansandan jihar Kano ta kama wata mata mai suna Aisha Kabiru yar shekara 17 sakamakon kashe makwabciyarta mai suna Bahijjah Abubakar yar shekara 28 a karamar hukumar Kumbotso. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da haka wa manema labarai. Ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar 21 ga watan Agusta.

Ya ce Aisha da Bahijjah sun yi fada, sai aka raba su. Amma daga bisani Aisha ta samo wuka mai tsini ta je ta caka wa Bahijjah a bayan wuyarta. Lamari da ya yi sanadin mutuwar Bahijjah bayan an kai ta Asibiti.

Aisha na fuskantar bincike a sashen CID na Shelkwatar yansandan jihar Kano. 

Ya ce za a gurfanar da ita a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE