Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Sako Daliban Makarantar Bethel Baptist KadunaYan bindiga sun sako ɗaliban makarantar sakandiren Bethel Baptist guda 15, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Idan zaku iya tunawa a bayan yan bindiga sun sako ɗalibai 28 daga cikin waɗanda suka sace ranar Lahadi 25 ga watan Yuli bayan an biya miliyan N50m kuɗin fansa.

Barayin sun sace adadin ɗalibai 121 a makarantar kamar yadda shugaban Baptist reshen Kaduna, Ishaya Jangado, ya bayyana, wanda shine ke jagorantar makarantar.

Shugaban ƙungiyar kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar Kaduna, John Hayab, yace yan bindigan sun sako ɗaƙibai 15 ranar Asabar da daddare, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Cikakken bayani zai biyo baya

Source: Legit.ng

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari