Da duminsa: Yan bindiga sun sako malamai da daliban kwalejin gona na Bakura a jihar Zamfara (Hotuna)


Yan bindigan daji sun sako dalibai da Malaman kwalejin koyon aikin gona da ilimin kimiyyar dabbobi na Bakura a jihar Zamfara.

Yan bindiga sun sace malamai 3 da dalibai 15 da kuma direban motarsu ranar 16 ga watan Agusta 2021 bayan Yan bindigan sun farmaki kwalejin.

TVC ta labarta cewa an kammala shirin ganin Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya gana da malamai da dalibai da Yan bindigan suka sace a gidan gwamnati da ke Birnin Gusau.
Previous Post Next Post