Duba yawan litar man fetur da Yan Najeriya ke sha a rana daya


Shugaban kamfanin NNPC a Najeriya, Mele Kyari ya ce ya umarci a binciki zargin sayarwa Najeriya lita miliyan 103 na man fetur a kullum a watan Mayu. BBC Hausa ta ruwaito.

Kyari ya shaida hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai kan kuɗaɗe.

Kwamitin a yanzu haka na sauraron bayanai kan kudaden da kamfanin ya kashe tsakanin 2022 zuwa 2024.

A lokacin da yake amsa tambayar kwamitin kan sayarwa ƴan najeriyar lita 103 na man fetur a kullum, Kyari ya ce za su binciki gaskiya zancen.

Ya kuma shaida cewa, idan akwai ranar da ake sayer ko shan lita miliyan 103 na fetur, bai sani ba. Amma ya diga ayar tambaya lokacin da aka gabatar masa da wadanan alkaluma. Ya ce babu shaka shi ya shaida hakan kwanaki uku da suka gabata, amma ya ce za su bincika.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari