Da Dumi-Dumi: Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N250


Yan bindigan da suka sace malamai da É—alibai a kwalejin fasahar noma da dabbobi dake Bakura, jihar Zamfara, sun nemi a basu miliyan N250m kuÉ—in fansa.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N250m kuÉ—in fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Mainasara yace:

"Sun faÉ—a mun cewa sai an basu kudin da suka bukata kafin su sako É—alibai da malaman da suka kwashe a makarantar da nake jagoranta."

Wa zai biya waÉ—annan makudan kuÉ—i?

Sai dai shugaban makarantar bai fayyace cewa iyalan waÉ—anda aka sace ne zasu biya waÉ—annan kuÉ—aÉ—en ko kuwa gwamnatin jihar Zamfara.

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Muhammad Shehu, yace sam hukumar yan sanda bata san É“arayin sun nemi kudin fansa ba.

Shehu yace:

"Bamu da masaniya game da bukatar yan bindigan na kuÉ—in fansa amma muna iyakar bakin kokarin mu wajen kubutar da gaba É—aya waÉ—anda aka sace."

Rahotun Legit News

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN