Buhari zai gana da shugabannin tsaro na Najeriya


Shugabannin Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a fadarsa a ranar Alhamis. BBC Hausa ta ruwaito.

Sanarwar da fadar shugaban na Najeriya ta fitar ta ce Buhari wanda ya dawo daga London a ranar Juma’a zai gana da shugabannin tsaron ne domin tsara tsare-tsaren kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da ke gabansu.

Sanarwar ta ce jami’an tsaron ƙasar sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da ƴan fashin daji da sauran masu aikata laifuka da suka addabi ƙasar waɗanda hakan ke sa suke miƙa wuya.

Ganawar ta ranar Alhamis a cewar sanarwar, ta shafi sanar da shugaban ƙasa kan ci gaban da aka samu.

Previous Post Next Post