$ads={1}
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kazalika mutanen sun kashe wani mutum mai suna Princewill.
$ads={1}
Wani ganau ya ce bayan mutanen sun kashe shugaban Yan Banga, sun kuma gundule kanshi daga gangar jikinsa.
Kafin mutuwar Ikechi, shi ne shugaban kungiyar Banga OSPAC wanda Gwamnati ta dakatar da ayyukanta a fadin jihar saboda wasu dalilan tsaro.
$ads={1}
Kakakin rundunar yansandan jihar Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an tura jami'an yansanda zuwa inda lamarin ya faru domin hana tabarbarewar lamarin zuwa ramuwar gayya.