Ana shirin yi wa ƴan arewa sakiyar da ba ruwa'


Shafin BBC Hausa ya wallafa rahotu cewa,  gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Najeriya ta yi zargin cewa kudurin dokar da `yan majalisar dokokin kasar suka zartar a kan inganta harkar man fetur na cike da wasu kura-kurai, wadanda za su iya cutar da al`ummar da ke yankin arewacin kasar.

Kungiyar ta ce ta hada kai da wasu kwararru wajen nazarin kudurin dokar, kuma ta fahinci cewa mai zai yi tsada a arewa fiye da kudancin kasar sakamakon dawainiyar da ke cikin dakonsa.

Ta ƙara da cewa tanadin da aka yi a cikin kudurin na amfani da kashi talatin cikin dari na ribar da kamfanoni za su samu wajen hakar mai a tudu ba zai biya muradin hakar mai a arewacin kasar ba, saboda haka bai kamata Shugaba Buhari ya sa hannu a kan kudurin dokar ba.

Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, Nastura Ashir Shariff, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun lura akwai zunzurutun rashin gaskiya da ban tsoro a cikinsa, don haka ba za su amince da shi ba.

''A zo a ce za a dauke wannan kasuwar man fetur a cire dukkan ma'aikatu uku da suke kula da farashin man nan a tattara a danka a hannun wani kamfani na wani dan kasa mutum daya, wannan akwai rashin adalci a ciki'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa babu abun da hakan zai haifar illa tsadar man fetur ga al'ummar arewa saboda sai an yi dakon man daga kudu za a kai yankin, abin da zai haifar da wahalarsa a arewacin Najeriya.

Ya ce: ''A cikin farashin man fetur din nan da ake siyarwa Naira 165 ko 167 ana biyan kusan fiye da Naira 8 a matsayin kudin da ake cirewa na dakon man fetur, ka ga babu gaskiya a ciki, kuma an tabbatar da cewa talaka za a cuta a ciki.''


''Mu kiranmu ga Shugaba Muhammadu Buhari shi ne kada ya yadda ya sa hannu a wannan doka, domin idan aka yi haka ba abun mamaki ba ne, misali, a rika sayar da lita Naira 10 a kudu, a arewa kuma Naira 25 ba''

Kungiyar ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar wa majalisar dokokin Najeriya wannan doka kamar yadda ya sha yi a baya, domin ta sake duba ta, ta yi abin da ya dace ga kowa da kowa.

''Shugaban kasa yana da ikon da zai yi haka, domin tabbatar da cewa ba a sayar da Najeriya ga 'yan kasuwa da 'yan jari hujja ba'' a cewarsa.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE