Usman Kyari, kanin Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda, ya zama a saman kanun labarai bayan jama'a sun kyalla ido sun ga irin hotunan rayuwarsa da yake wallafawa a shafinsa na Instagram.
Hankali ya koma kan Usman ne bayan Hushpuppi, wanda aka fi sani da Ramon Abbas, ya ce ya baiwa Abba Kyari wasu makuden kudaden domin ya kama wani dan damfara abokin hamayyarsa.
Kafin aukuwar wannan lamarin, an san babban dan sandan da zama koyaushe a kafar sada zumunta ta Instagram.
Idan baya wallafa hotunan jarumtarsa a yayin da yake ragargazar 'yan ta'adda, toh tabbas za a ganshi ya choge cikin 'yan uwansa, manyan 'yan siyasa da fitattun jama'a, thecable ta ruwaito.
Kamar dakataccen dan sandan, shafin Usman na Instagram dankare yake da son shanawa tare da fantamawa cikin arziki karara, thecable ta ruwaito
Daga daukan hotuna cikin jerin motocin alfarma zuwa sanya kayan alfarma na sutura, sharinsa yana da mabiya sama da 2,000 na masu son ganin kyale-kyale.
Source: Legit