Yadda PDP da APC suka caccaki Farfesa Jega kan gargaɗin da ya yi wa 'yan Najeriya, duba abin da ya ce


BBC Hausa ta ruwaito cewa jam'iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya a Najeriya sun mayar wa tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC) na ƙasar martani game da kalamansa da ya yi cewa sun gaza kuma "kar 'yan Najeriya su sake zaɓen su".

Cikin wata hira da BBC Hausa ranar Litinin, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa "APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba", yana mai cewa ya shiga jam'iyyar PRP.

"Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa ɓarayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaɓa sun koma APC, kuma shiru kake ji," in ji shi.

A cewarsa: "Shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya."

Dukkan APC da PDP babu wadda ta yarda da maganar tsohon shugaban INEC ɗin cewa ta gaza wajen kyautata rayuwar `yan Najeriya ballantana a ce kar a zabe ta a nan gaba.

Martanin PDP

Babbar jam`iyyar hamayya ta PDP ta yi iƙirarin cewa ta cimma nasarori masu ɗimbin yawa a lokacin da APC ta ƙwace mulki daga hannunta, saɓanin matsain rayuwar da `yan kasar ke fama da shi a halin da ake ciki.

PDP ta ce ba ta musanta cewa APC ta gaza ba amma idan har za a yi ƙwaƙwa, to tsohon shugaban hukumar zaben ma da nasa laifin, saboda da shi aka yi uwa da makarbiya wajen bai wa APC nasara a lokacin da ta yi wa PDP kaye.

Mista Kola Olagbondiyan, shi ne Sakataren Yaɗa labaran PDP, kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa abin takaici ne yadda Jega ya nuna "rashin fahimtarsa a fili" a matsayinsa na farfesan kimiyyar siyasa.

"Ya kamata a tunasar da Farfesa Jega yadda PDP ta haɓaka tattalin arzikin Najeriya, ta biya tulin bashin da ake bin ta...har ma tattalin arzikinta ya zama ɗya daga cikin mafiya haɓaka cikin sauri kuma cibiyar zuba jari mafi girma a Afirka.

"Amma sai APC ta zo ta lalata shi sannan ta mayar da ƙasarmu babban birnin talauci na duniya da kuma cin bashi a cikin shekara shida."

Martanin APC

Ita ma jam`iyyar APC a nata martanin, ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP da bar mata, tana mai cewa abubuwan da Shugaba Buhari ya cimma "zarta na PDP".

Ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP ta bar mata, wadanda take fadi-tashin gyarawa,

Kazalika, ta yi wa Farfesa Jega ba'a tana mai cewa watakila yana jiran ta yi masa tayi ne tun da ya shiga siyasa.

"Idan jam'iyyar APC ya ke so ya shigo to sai ya zo ofis ɗin ɗinmu ya karɓi takardu ya karanta domin ya fahimta sosai ya shigo," in ji Daraktan Yaɗa Labaran APC na Ƙasa, Mallam Salisu Na`inna Danbatta.

Sai dai ya ce Farfesa Jega ya yi gaskiya kan abubuwan da ya faɗa a kan PDP.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN