An damke barawon manyan wayoyin wuyar lantarki a jihar Arewa


Rundunar yansandan jihar Adamawa ta kama wani matashi mai suna Haruna  Muhammed mai shekara 29 bisa zargin satar manyan wayoyin wutan lantarki a karamar hukumar Mubi ta kudu.

Kakakin hukumar yansandan jihar DSP Suleiman Nguroje ya ce an kama Haruna wanda dan asalin Angwan Kara a Mubi ta kudu ne bayan ya aikata satan kuma ya je ya boye a maboyarsa da ke Mugulvu a bayan wata Makabarta yana jiran abokan harkallarsa.

Sakamkon harkar sace sacen wayoyin lantarki da Haruna da abokan harkallarsa ke yi ya sa suka jefa jama'ar Maiha, Mubi da garuruwa da ke makwabtaka cikin matsalar wutan lantarki.

Yansanda na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su maka Haruna a wata Kotu domin ya fuskanci hukunci a cewar Kakakin rundunar yansandan jihar Adamawa. 


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari