Bayan dakatar da Abba Kyari daga aikin dansanda, an fara bincikensa


Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT daga gudanar da ayyuka da ayyukan ofishinsa, Vanguard ta ruwaito.

Wata sanarwa da Ikechukwu Ani, Babban jami'in Hulda da Jama'a ya ce:

"Dakatarwar Abba Kyari ta fara aiki daga ranar Asabar, 31 ga Yuli, 2021 kuma za ta ci gaba da jiran sakamakon bincike dangane da tuhumar da Ofishin Binciken Tarayyar Amurka ya yi.

“Hukumar ta kuma umarci Sufeto Janar na 'yan sanda da ya ba ta bayanai kan ci gaba kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Hukuncin hukumar na dauke ne cikin wata wasika mai lamba PSC/POL/D/153/vol/V/138 dauke da kwanan watan yau Lahadi, 1 ga watan Agustan 2021.

An zargi Abba Kyari da taimakawa Abbas Ramon wanda ake kira Hushpuppi, inda rahoton hukumar FBI ta kasar Amurka ta bayyana cewa, ya karbi cin hanci a hannun Hushpuppi.

Sai dai, kafin dakatarwar, Biyo bayan takaddamar da aka samu daga rahoton Amurka da ke tuhumar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DSP), Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda (PSC) a ranar Asabar, 31 ga Yuli ta yi martani kan takaddamar.

Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ba ta sami rahoto na doka ba kuma mai ma'ana kan "bakon" zargin na Amurka mai umarnin kama Abba Kyari.

Legit.ng ta tattaro cewa PSC ta yi kira ga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ya jagorance ta kan batun tunda ita (hukumar) ita ce hukumar da ke da ikon ladabtar da jami'an 'yan sanda da suka yi kuskure.

IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki

A baya kadan, Sufeton 'Yan Sandan IGP Usman Alkali Baba, ya nemi a 'gaggauta' dakatar da Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa kwanakin nan da ke da alaka da dan damfarar nan Abbas Roman Hushpuppi.

Baba, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Frank Mba ya fitar, ya ba da shawarar dakatar da Kyari nan take inda aka fara bincike akansa, in ji rahoton Daily Trust.

IGP ya kafa wani kwamati na mutum hudu karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike domin bincikar zargin da ake yi wa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta 'yan sanda wato IRT.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN