Yanzu-Yanzu: Ministan Shugaba Buhari Ta Yanke Jiki Ta Faɗi a Wurin Taro


Ƙaramar minitan ma'aikatun kasuwanci da hannun jari, Maryam Yalwaji Katagun, ta yanke jiki ta faɗi a wurin wani taro a jihar Bauchi ranar Litinin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ministan, wanda taje Bauchi domin ƙaddamar da wani shirin bada tallafi, ta yanke jiki ta fafi ne yayin da take ƙoƙarin jawabinta ga mahalarta taron, wanda mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela, yana wurin.

An gaggauta ɗaukar ministan zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa Bauchi (ATBU-TH).

"Ba zato ba tsammani ta riƙe ƙanta, ta faɗi ƙasa a hankali, yayin da jami'ai suka yi gaggawar ɗaukarta zuwa Asibiti." inji wani shaidan gani da ido.

Ministan ta kai ziyarar aiki Bauchi tun ranar Asabar

Legit.ng hausa ta gano cewa ministan, wanda ta kasance a jihar Bauchi tun ranar Asabar, ta yi fira da gidan radiyon Globe FM a wani shirin kai tsaye ranar Lahadi.

Hakanan kuma ta gudanar da wasu ayyukan tun bayan zuwanta jihar kafin taron ƙaddamar da tallafi ranar Litinin.

Duk wani ƙoƙari na jin halin da take ciki a cibiyar kula da masu rauni na ATBU-TH yaci tura.

Amma wani babban jami'in gwamnati ya shaidawa manema labarai cewa da zaran ta samu dauƙi zats koma Abuja domin a cigaba da kulawa da lafiyarta.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN