Lamari ya yi zafi: Sarkin Yarbawa ya shawarci Sunday Igboho ya mika kansa ga DSS


Ya jaddada a taron majalisar sarakunan gargajiyan yankin cewa, babu wanda ya taba tattauna batun ballewa kuma sarakuna sun yi imani da hadin kan kasar nan.

Oba Makama ya ce:

“Babu wata gwamnatin da za ta so ta ga kasarsa cikin rikici. Yakin neman ballewa daidai yake da amfani da makamai don yakar kasa.

“Babu wanda ya isaya kalubalanci gwamnati kuma ya yi nasara. Najeriya ba za ta zauna ba, bayan yakin basasa, kuma ta sake fuskantar wani yakin cikin gida.

“Yan bindiga da 'yan Boko Haram da muke dasu yanzu sun isa. Don haka, zan ba masu fafutukar ballewa shawarar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya

“Sunday Igboho ya kamata ya mika kansa ga gwamnati bisa son ransa. Za a ji tausayinsa maimakon su kamashi.”

Ya kara da cewa:

“Maimakon kira ga ballewa, zan goyi bayan sake fasalin kasa saboda idan aka sake tsari, to za a iya mika mulki. Idan aka karkata akalar mulki, za a samu karin kudi.

Sunday Igboho Ya Tura Sako Ga FG, Yana Neman Diyyar Makudan Kudade

Sunday Igboho a ranar Asabar ya rubuta takardar koke ga gwamnatin tarayya kan barnar da aka yi wa gidansa, motoci da sauran kadarori da jami'an tsaro suka yi, The Nation ta ruwaito.

Ya yi kiyasin asarar da ya yi cewa ya kai Naira miliyan 500 kuma ya nemi a biyashi wannan kiyasi.

Igboho, a cikin wata wasika ta hannun mai ba shi shawara Cif Yomi Alliyu (SAN) ya kuma nemi gafara daga jama'a kan abin da ya kira take hakkinsa da aka yi a lokacin da aka mamaye gidansa da kuma wani binciken da jami'an tsaro suka yi.

An Kame 'Yan Gangamin Kafa Kasar Yarbawa 47 Dauke da Layu, Zasu Bayyana a Kotu Gobe

A wani labarin, A wani labarin daban, Jihar Legas - A rahoton da Legit.ng Hausa ta samo, rundunar 'yan sanda ta jihar ta cafke wasu daga cikin masu gangamin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa a yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a jiya Asabar a cikin jihar.

Bayan tabbatar da kamun, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu ya gabatar da wasu mutane 47 da aka kama a wurin zanga-zangar ta nuna goyon baya ga kafa haramtacciyar kasar Yarbawa.

An gabatar da hotuna, mazuban abinci, layu, da sauransu a matsayin abubuwan da aka kame yayin zanga-zangar.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN