Majalisar jihar Kano ta dakatar da Riminado shugaban hukumar kula da almundahana na jihar, duba dalili


Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da Mahuyi Magji Rimingado, shugaban hukumar kula da bincike da koken jama'a  na jihar watau, Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission. 

Wannan ya biyo bayan wata takardar koke ne da Akanta janar na jihar ya aika wa Majalisar dokokin na jihar Kano yana zarginsa da rashin da'a.

An dakatar da Rimin Gado har tsawon wata daya domin a gudanar da bincike.

Majalisar ta umarci shugaban Kwamitin kula da koken jama'a Hon Umar Musa Gama, ya jagorancin binciken, kuma ya gabatar da rahotunsa a cikin mako biyu.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN