Samari sun kashe bawan Allah garin kokuwan kwace wayarsa a karkashin gadar Kantin kware da dare


An kashe wani mutum dan shekara 40 mai suna Umar Muhammad Ahmad Wanda ake zargin gungun wasu barayin waya ne suka kashe shi a birnin Kano ranar Asabar.

Kafin rasuwarsa, Umar Muhammad ma'aikacin hukumar kula da gidajen tarihi ne watau National Commission for Museum and Monument, ofishin Kaduna.

Wata majiya a unguwar Fagge, da bata son a ambaceta, ta ce Umar ya gamu da ajalinsa ne da dare lokacin da yake takawa da kafa zuwa gida ta karkashin gada a Kantin kwari. Sai wasu samari suka fuskance shi da kokuwa domin su kwace wayarsa. Daga  bisani daya daga cikinsu ya daba masa wuka lamari da ya haifar da matsanancin zubar jini. Su kuma samarin sai suka tsere tare da wayarsa da suka kwace.

An garzaya da Umar zuwa ofishin yansanda na Kofar wambai a sume, inda aka shigar da kara, kuma aka kai shi Asibitin Abdullahi Wase inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

An bizine Umar a birnin Kano ranar Asabar. Ya rasu ya bar mata guda da yara uku.

Kwace wayar salula tare da kashe masu wayar a birnin Kano ya Zama ruwan dare, duka da kokarin da yansanda ke yi wajen kama barayin wayar kuma suna gurfanar da su a gaban Kotu. Amma duk da haka lamarin sai karuwa yake yi a birnin Kano.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN