Yadda Sheikh Abduljabbar Kabara ya shafe daren farko a hannun 'yan sanda


Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na jihar Kano Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya shafe daren farko a hannun rundunar yan sandan jihar.

Tun da farko kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC Hausa cewa sun gurfanar da malamin a gaban wata kotun shari'ar musulunci da ke jihar, wadda ita ce ta bukaci 'yan sanda su ci gaba da rike shi, kafin ranar litinin da za a mayar da shi gidan yari.

An gurfanar da malamin ne a ranar Juma'a, bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar, ta ce an gurfanar da Malamin ne, "wanda ya yi ƙaurin suna wajen yin wa'azin da kan haifar da muhawa, saboda zargin furta kalaman da ka iya haifar da tunzuri, da kuma bata sunan Annabin Allah''.

Kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 28 ga wannan watan na Yuli domin ci gaba da sauraron shari'ar.

Malamin zai ci gaba da zama karkashin kulawar 'yan sanda har zuwa ranar Litinin da za a kai shi gidan yari, kafin lokacin da za a ci gaba da sauraren shari'ar tasa, kamar yadda kotun ta buƙaci a yi.

Matashiya

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka gudanar da muƙabala tsakanin Malamin da sauran Malaman Jihar Kano bisa bukatarsa ta ƙalubalantarsu kan da'awarsa wadda suke ganin ba daidai yake ba.

An yi wa Malamin tambayoyi da dama amma ya gaza amsa wa, inda yake ta nanata cewa mintinan da ake ba shi domin ya yi bayanin da'awarsa sun yi masa kaɗan.

Haka dai aka kammala wannan muƙabala ba tare da ya yi bayanin da ya gamsar da malaman da ya nemi zaman muƙabalar da su ba.

Daga baya ya fitar da wani bidiyo wanda a ciki ya nemi afuwar mabiyansa da duk wanda abin ya bata masa yana cewa duk abin da yake yi yana yin sa ne min kare mutuncin ma'aiki.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN