Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Igangan, Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro


Wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun sake kai hari Igangan, ƙaramar hukumar Ibarapa ta arewa, jihar Oyo, da daren ranar Jumu'a, inda duka kashe mutum huɗu, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Sai dai jami'an tsaron sa kai na yankin sun samu nasarar fatattakar maharan kafin su yi mummunar É“anna.

Kwamandan jami'an tsaron Amotekun a ƙaramar hukumar Ibarapa, wanda aka bayyana sunansa da Muri, ya na daga cikin waɗanda suka rasa ransu.

Yan bindiga sun sake kai hari Igangan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Igangan, Sun Hallaka Kwamandan Jami'an Tsaro Hoto: thenationonlineng.net

Yan bindiga da kayan sojoji da na kwastam

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kai hari garin ne a cikin motar Hilux guda biyu, motar bus mai É—aukar mutum 18, da kuma Toyota Sienna, suna sanye da kayan sojoji da kwastam.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan sun shigo garin da É—umbin yawa amma ba zai iya faÉ—in adadinsu ba.

Wani sananne a garin Igangan, Oladiran Oladokun, ya tabbatar da harin, yace wannan farmakin wani ƙoƙarine na mamaye jihar amma jami'an tsaron sa kai na yankin suka daƙile shi.

Oladukon yace maharan sun zo cikin kayan sojoji da kwastam domin su yaudari mutanen gari, daga baya su canza lamarin.

Ya kuma bayyana rashin jin daɗinsa bisa rashin tsaro a yankin duk da ƙalubalen kawo hari da ake fuskanta.

Sun kashe kwamandan Amotekun

Wani shugaba a yankin, wanda ya yi jawabi cikin yaƙini, ya bayyana cewa:

"Na samu rahoton cewa da misalin ƙarfe 8:00 na dare wasu yan bindiga da ake zargin fulani ne sun kai hari Igangan, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi na tsawon minti 30."

"Wasu mutane sun ce jami'an kwastam ne saboda sun sanya kayan jami'an, amma jami'an tsaron sa kai da mafarauta sun fatattake su."

"Maharan sun bi ta ƙauyen Igboora suna harbi kan mai uwa da wabi, sun kashe wasu mutane a can ciki harda kwamandan jami'an tsaron Amotekun."

Da aka tuntuɓi wani jami'in Amotekun, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa jami'ai sun maida martani cikin gaggawa inda maharan suka tsere, amma sun kashe wasu mutane.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi , ya bayyana cewa za'a ɗauki mutum 20,000 da zasu yi aiki a tashoshin jirgin ƙasa dake layin Kaduna-Kano.

Ministan yace ma'aikatarsa zata cigaba da aiki ba dare ba rana domin cika umarnin shugaba Buhari na zamanantar da layin dogo.

Source: Legit

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN