Rundunar 'yan sanda ta kama Sheikh Abduljabbar


Rundunar 'yan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa ta kama Malamin nan Sheik Abduljabbar Kabara.

Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya gaya mana cewa sun gurfanar da Sheik Abduljabbar a gaban kotun Kofar Kudu da ke kwaryar Birnin Kano a ranar Juma'a, bisa zargin ɓatamci ga addini da kuma tunzura jama'a.

A cewarsa tuni alƙali ya aike da shi gidan yari.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammad Garba ya fitar ta ce an gurfanar da Malamin ne, "wanda ya yi ƙaurin suna wajen ɓatanci ga manzon Allah da kuma Sahabbansa", bayan da aka samu rahoton farko daga wurin 'yan sanda da kuma ofishin kwamishinan shari'a wadanda suka shirya tuhume-tuhumen da ake yi wa Malamin.

"An gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu da ke kofar kudu a ranar 16 ga watan Yuni, inda Alkali Ibrahim Sarki Yola, ya karanto masa laifukan da ake tuhumarsa da su wandanda suka haɗa da batanci ga addini da tunzura al'umma da kuma wasu sauran laifuka," in ji sanarwar.

Kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 28 ga wannan watan na Yuli domin ci gaba da sauraron shari'ar.

malamin zai ci gaba da zama karkashin kulawar 'yan sanda har zuwa ranar Litinin da za a kai shi gidan yari, kafin lokacin da za a ci gaba da sauraren shari'ar tasa.

Matashiya

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka gudanar da muƙabala tsakanin Malamin da sauran Malaman Jihar Kano bisa bukatarsa ta ƙalubalantarsu kan da'awarsa wadda suke ganin ba daidai yake ba.

An yi wa Malamin tambayoyi da dama amma ya gaza amsa wa, inda yake ta nanata cewa mintinan da ake ba shi domin ya yi bayanin da'awarsa sun yi masa kaɗan.

Haka dai aka kammala wannan muƙabala ba tare da ya yi bayanin da ya gamsar da malaman da ya nemi zaman muƙabalar da su ba.

Daga baya ya fitar da wani bidiyo wanda a ciki ya nemi afuwar mabiyansa da duk wanda abin ya bata masa yana cewa duk abin da yake yi yana yin sa ne min kare mutuncin ma'aiki.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN