Yadda matashi ya kashe mahaifinsa a gona ya sayarwa matsafa hannaye 2 da zuciyarsa a jihar Arewa


Hukumar yansandan jihar Kwara ta kama wani mutum bayan ya kashe mahaifinsa mai suna Michael Olagunju, kuma ya sayarwa matsafa sassan jikinsa a garin Kajola, Odo-Owa da ke karamar hukumar Oke-Ero.

Olagunju ya rasa ransa bayan dansa ya hada baki da wasu matsafa suka yi masa kisan gilla a cikin gonarsa kuma ya sayar wa matsafan sassan jikin mahaifinsa. Daga ciki har da hannayensa guda biyu da zuciyarsa.

Kakakin hukumar yansandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce yansanda na gudanar da bincike. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN