Duba abin da ya faru wajen zanga zanga don kafa kasar Yarbawa a Lagos


Rahotanni na cewa an kashe wata matashiya a wurin zanga-zangar masu son kafa ƙasar Yarabawa yau Asabar a Jihar Legas da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna gawar yarinyar rufe da wani mayafi kwance a ƙasa cikin jini.

Kazalika, wani mutum wanda babu tabbas ko shi ne yake ɗaukar bidiyon, an ji shi yana cewa harsashi ne ya kashe yarinyar a lokacin da take yin sayayya a wani shago.


Rahotanni sun nuna cewa an ji ƙarar harbin bindiga yayin da 'yan sanda ke ƙoƙarin tarwatsa mutanen.

Mutane a bidiyon na cewa shekarar yarinyar 14 da haihuwa.

Lamarin ya faru ne a wurin shaƙatawa na Gani Fawehinmi Freedom Park wanda ke kusa da inda ake zanga-zangar.

Yan sanda na tarwatsa masu zanga-zangar kafa ƙasar Yarabawa a Legas

Legas

'Yan sanda a Jihar Legas sun yi amfani da ruwa domin tarwatsa masu zanga-zangar neman kafa ƙasar Yarabawa.

Ana gudanar da zanga-zangar ce a Ojota, inda masu macin suka taru ɗauke da kwalaye masu rubutun goyon bayan ɓallewa daga Najeriya.

A ranar Alhamis ne hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce jami'anta sun kai sumame gidan jagoran zanga-zangar mai suna Sunday Adeniyi Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho da ke garin Ibadan na Jihar Oyo.

Hukumar ta ce ta tura jami'an nata ne sakamakon samun bayanan sirri da ke nuna cewa ya tara makamai a gidan, inda ta ce ta kashe uku cikin mutanensa masu ɗauke da bindiga tare da kama wasu da kuma makamai da ta samu a gidan.

Sai dai duk da umarnin haramta zanga-zangar da 'yan sanda suka bayar, mutanen sun fito a yau Asabar domin bayyana ƙudirinsu.

Rahotun BBC

Social embed from facebook

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN