Rundunar yansandan jihar Adamawa ta kama wata matar aure mai suna Aisha Muhammed, yar shekara 18 bisa zargin azabtar da diyar kishiyarta mai shekara 5 bayan ta tura mata karfe mai zafi a alaura saboda ta yi fitsarin kwance.
Mun samo cewa Lamarin ya faru ne a kauyen Wuro Patuji da ke karamar hukumar Mubi ta kudu a jihar Adamawa.
Kakakin hukumar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje, ya shaida wa manema labarai ranar Juma'a 2 ga watan Yuli cewa wadda aka kama ta yi amfani da karfe mai zafi ta tura a al'aurar karamar yarinyar. Lamari da ya raunata ta, kawai domin ta yi fitsari a kwance.
Ya ce mahaifin yarinyar ya saki mahaifiyar yarinyar, sakamakon haka kishiyar uwar watau Aisha take kula da yarinyar.
Ya kara da cewa mahaifiyar yarinyar da wata Lauya ta shigar da rubutaccen kara ga yansanda. Sakamakon haka yansanda suka cafke Aisha kuma suna gudanar da bincike.