Yadda magidanta 2 suka yi canjen matansu na aure domin su sasanta matsalar da ke tsakaninsu


Wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo ya faru bayan wasu magidanta biyu sun yi canjen matansu na aure domin su kawo karshen matsala da ke tsakaninsu.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa Josh Odour da Sakis wadanda ke zaune a gundumar Busia da ke yammacin kasar Kenya sun yi canjen matansu har da diyansu. Bayan Sakis da matar Odour sun fallasa lamari da ke tsakaninsu. A cewar KDRTV, da farko Odour ya sami gulmace gulmacen cewa matarshi tana nema da Sakis, amma bai yarda ba.

Sai dai wata rana Odour ya kai ziyarar bazata gidan Sakis, sai ya tarar da matarsa tana wanke kwanukan abinci da ayyuka irin na zaman aure a cikin gidan. Sakamakon haka Odour ya je ya lallashi matar saki wacce ita ma dama ta yi yaji ta koma gidansu. Daga bisani shi ma ya tafi da ita gidansa ya ci gaba da zaman aure tare da ita. 

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN