Ni ke shugabancin jihata, Zulum ya karyata rade-radin kafa gwamnan Boko Haram a Borno


Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya musanta rahoton dake yawo na nada gwamna a wasu yankunan jihar Borno da Boko Haram tare da ISWAP suka yi.

A makon da ya gabata, bidiyon da ake zargin na nada gwamnan Boko Haram a Borno ne ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Daily Trust ta ruwaito.

Hukumar rikon kwarya ta 'yan ta'addan ta samu shugabancin wani Abba Kaka, wanda aka nada a matsayin shugaban wasu yankunan Borno.

Amma yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, gwamnan ya karyata wanna labarin, Daily Trust ta wallafa.

Ya jaddada cewa "shi ke jagorantar jiharsa."

Zulum yace mulkinsa baya bincikar al'amarin

"Har yanzu bamu fara bincikar sahihancin rahoton nada gwamnan Borno da 'yan ta'adda suka yi ba. A matsayina na gwamnan jihar, a tunani na bai dace in yi magana kan abinda bani da iliminsa ba cikakke."

Rahoton bashi da sahihanci, a kafar sada zumunta. 

A yayin da aka tambaya gwamnan ko zai yi bincike, Gwamna Zulum yace a'a, ya dora laifin rahoton ga kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa: "Ba zan yi bincike ba saboda rahoton bashi da sahihanci. Rubutu ne kawai kuka gani a Facebook. Ku 'yan jarida ne, ina tunanin sai mun san ingancin rahoto kafin mu yi tsokaci a kai.

"Ni dai abinda na sani shine, ni ne gwamnan jihar Borno kuma bani da wani labari na cewa akwai wata gwamnati ta daban. Tabbas ni ke shugabantar jihar."

A wani labari na daban, diyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua da mijin tsohuwar matar gwamnan Taraba, Hauwa Suntai suna shari'a kan wani fili dake yankin Kado a babban birnin tarayya na Abuja.

PRNigeria ta tattaro cewa Zainab Yar'Adua tsohuwar matar tsohon gwamnan Kebbi, Saidu Dakingari, ta bayyana cewa fili mai adireshi 506, Cadastral Zone B09, yankin Kado a babban birnin tarayya Abuja.

Duk da kamfaninta mai suna Marumza Estate Development Company Limited, Yar'Adua ta maka wani kamfani mai suna Itban Global Resources Limited da kuma shugabanshi, Halliru Saad Malami a gaban kotu tare da ministan Abuja kan rikicin filin.

Rahotun Legit

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE