Tsohon gwamnan Kano, kuma Sanata mai wakiltar Kano Ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwa a kan yadda wasu 'yan siyasa a jihar ke ƙoƙarin farfaɗo da siyasar daba da aka jima da kawar da ita.
Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Sashen Hausa na BBC, inda ya ce babbar illa ce a ci gaba da yin hamayyar siyasa a Kano kamar yadda ake ganin wasu na yi, ta hanyar ɗaukar makamai suna far wa abokan hamayyarsu.
Yana magana ne kan batun fitar da wanda zai gaji gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje a zaɓen 2023, inda ya ce akwai bukatar shugabannin jam'iyyar APC na jihar su yi wa kowa adalci, kada a hana duk mai sha'awa tsayawa takara.
Ya ce "Babu laifi masu neman mukamai su fito, yau in masu neman gwamna sun kai mutum 100 karkashin jam'iyyar APC a Kano duk su fito, abun da kawai muke ganin zai zama illa shi ne ya zamana ana siyasar gaba, wannan ƙauyanci ne, shirme ne, kuma ya saɓa wa tarbiyyar addinin Musulunci ma", in ji shi.
Alakar majalisa da gwamnatin Buhari
Sanata Ibrahim Shekarau ya kuma taɓo batun da ya shafi alakar majalisarsu ta dattawan Najeriya da gwamnatin shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, inda ya ce sabanin majalisar da ta gabata, a yanzu an samu kyakkyawar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu, don haka suna aiki tare don ciyar da Najeriya gaba.
''Wancan zango majalisa ta 8 kowa ya ga rigingimun da aka yi, sai a shekara ana rigima, amincewa da kasafin kudi ma ya gagara, fahimtar juna ma ta gagara, to amma wannan majalisa ta fahimci cewa ba wannan ne mafita ba", a cewarsa.
Ya kuma mayar da martani ga masu cewa majalisar tasu ta zama ta 'yan amshin-shata la'akari da yadda ake ganin ba ta tanka wa gwamnati, inda ya ce sun sha fada wa gwamnati gaskiya a kan abubuwa da dama da suka shafi ƙasar.
"Ba daidai ba ne a fadi haka, domin an ga irin illar da aka samu a baya, mun sha fadar maganganu na gaskiya ga wannan gwamnati, an dade ana soki-burutsu kan abun da ya shafi kasafin kudi na shekara, muka lashi takobin ganin sai an dawo da tsarin Janairu zuwa Disamba, don wannan yana ba wa 'yan kasuwa damar daidaita tsarinsu da kasa, shugaban majalisa ya tsaya tsayin daka har sai da ya ga fadar shugaban kasa ta amince da shi.
Matsalar tsaro
Fitaccen ɗan siyasar na Najeriya ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare, da kan janyo rasa rayukan jama'a a jihohi da yankunan kasar daban-daban.
Ya ce ''Ko kiyashi ake kashewa ka ji an ce kullum an kashe 50 an kashe 100 za ka ji tausayi, za kuma ka ji cewa ba a kyauta ba ana sace mutane wasu ma ana kashe su, wasu ma har da yara kanana, wannan ba karamin tashin hankali ba ne''.
Sai dai ya ce babbar matsalar da ta janyo sukurkucewar harkar tsaro a Najeriyar na da nasaba da rashin adalci, don haka yi wa kowa adalci ne kadai zai shawo kan matsalar da ake fama da ita.
Sannan ya bukaci gwamnati ta samar da wani tsari da jama'a za su dauki gabarar kula da tsaronsu, inda ya bayar da misali da hukumar Hisbah da ya kafa a jihar Kano lokacin da yana gwamnan jihar, inda ya ce ta taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro da lalacewar tarbiyya a jihar.
Rahotun BBC