Yadda maigida ya yi wa matarshi dukan ajali saboda ta tambaye shi N1000 da ya ara a wajenta


Rundunar yansandan jihar Adamawa ta kama wani ma'aikacin gwamnati mai suna Usman Hammawa, mai shekara 41 a Duniya  bisa zargin yi wa matarsa mai shekara 36 a Duniya duka har ta mutu,

Kakakin hukumar yansandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da aukuwan lamarin a wata takarda da ya fitar ga manema labarai. Ya ce an kama wanda ake zargin ne ranar Talata 22 ga watan Yuli a karamar hukumar Ganye.

Ngoroje ya ce Usman Hammawa ya fusata ya fada wa matarsa da duka kuma ya buga kan matarsa mai suna Rabiyatu Usman da bango saboda ta tambaye shi Naira 1000 da take binshi bashi. Usman da Rabiatu sun shafe shekara 16 tare kafin Usman ya zama ajalinta a zamantakewar aurensu.

Sakamakon haka Rabiatu ta fadi ta suma kuma aka garzaya zuwa asibiti da ita inda aka tabbatar da mutuwarta.

Usman yana da yara biyar tare da Rabiatu kafin ya kasheta. Tuni yansanda suka fara binciken kwakwaf kan lamarin yayin da suke rike da Usman a wajensu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN