Hotuna: Harbe harben bindiga, tawagar Amurka sun tsere a wajen bikin binne shugaban Haiti


Masu zanga zanga a wajen bikin binne shugaban kasar Haiti da aka kashe sun yi harbe harbe da bindigogi suna ambaton Adalci ! Adalci !!.

Lamari da ya sa tawagar kasar Amurka a wajen bikin suka tsere. Gaba daya yanayin wajen bikin ya hargitse da fargaba.

Sai dai an ga Martine, matar tsohon shugaban kasar da aka kashe ta iso wajen bikin kuma ta zarce kai tsaye zuwa akwatin gawar mijinta, ta aza hannunta na hagu a kan akwatin gawar mijinta sai ta dora a zuciyarta yayin da ta tsaya shiru na wani lokaci idanunta cike da hawaye.

Bayan wasu mintoci gungun wasu magoya bayan tsohon shugaban kasar ta Haiti sun dauki wani babban hotonsa suka yi fareti yayin da yansanda suka kada ganga.

Idan baku manta ba, wasu mutane suka kutsa cikin gidan shugaban kasar Haiti kuma suka kashe shi bayan sun yi ta harbe harbm mako biyu da suka gabata. 
Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari