Uwargida ta kitsa sace kanta da taimakon maigidanta suka karbi N1m kudin fansa wajen mahaifinta


Rundunar yansandan jihar Niger ta  gurfanar da warta matar aure mai suna Safiya Ibrahim Umar tare da maigidanta mai suna Mohammed Mohammed bayan sun hada baki ta kitsa sace kanta da kanta.

Kakakin hukumar yansandan jihar Niger DSP Wasiu Abiodun ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a Mina babban birnin jihar Niger. Ya ce wadanda aka kama suna zaune ne a karamar hukumar Chanchaga, amma aka kamasu ranar 22 ga watan Yuli a unguwar Kimawa dake birnin Minna.

Ya ce an sanar da cewa an sace Sadiya a kan hanyar dawowa daga aiki a hanyar tsohuwar filin saukar jirage ranar  15 ga watan Yuli. Sadiya tana aiki a Makaratar Umar Bin Khattab International School Maitumbi.

Ya ce ranar 16/07/2021 wani ya tuntubi mahaifin Sadiya a wayar salula ya nemi fansar naira miliyan biyar kan Sadiya, ammam daga bisani aka rage kudin zuwa naira miliyan daya. An kai kudin a unguwar Rafin Yashi inda aka bukaci a je a ajiye kudin, yankin da ke cikin karamar hukumar Bosso daga wajen birnin Minna.

Ya ce sai dai ranar 21/07/2021 kwatsam sai ga Sadiya ta dawo da karfe 10 na dare. Daga bisani yansanda suka gayyace ta domin ta amsa tambayoyi.

Ya ce ta gaya wa yansanda gaskiya cewa sun hada baki da mijinta ne suka ce an sace ta domin su karbi kudin fansa daga mahaifinta. Ta ce mijinta ya kaita kauyen Nugupi ta hanyar karamar hukumar Paiko inda aka boyeta a wajen wani aminin maigidanta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN