Kotu ta dage shari'ar kara da dan kabilar Igbo ya shigar kan Hisbah, Atoni janar, da Kwamishinan yansandan jihar Kebbi


Babban Kotun tarayya da ke zamanta a garin Birnin kebbi ta dage sauraron shari'ar da wani dan kabilar Igbo ya shigar kan Atoni janar kuma Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi, Kwamishinan yansandan jihar Kebbi da hukumar Hisbah na jihar Kebbi.

Dan kabilar Igbo mai suna Onyebuchi Okafor ya sami wakilcin Lauyoyi guda uku karkashin jagorancin Lauya mai zaman kansa E.C Eugolina.

Lauyoyin Onyebuchi suna kalubalantar Atoni janar kuma Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi, Kwamishinan yansanda da hukumar Hisbah na jihar Kebbi bisa zargin cin zarafinsa, kuma yake neman Kotu ta sa su biya shi wasu miliyoyin naira. 

Sai dai bayan wata gajeruwar muhawara ta bangaren doka, sakamakon bayanai da takardu da ke gaban Kotu. Alkalin Kotun ya gano cewa wata Kotun Majistare da ke da hurumi a ƙarƙashin jihar Kebbi ne ta tasa keyar Onyebuchi zuwa gidan gyara hali.

Ya bukaci Lauyoyin Onyebuchi cewa su gabatar wa Kotunsa ayoyin doka da zai gamsar da Kotu ko akwai hurumin yiwuwar babban Kotun tarayya ta jinginar da umarni ko shari'ar da ke gaban Kotun Majistare na jiha kan Onyebuchi. Amma Laujoyin basu bayar da bayani ba.

Sakamakon haka, Alkalin Kotun ya yi umarni cewa su kawo wa Kotu rubutaccen gabatarwa da bayanai na da'awarsu kan hurumi. Daga bisani Alkalin Kotun ya dage zaman Kotu har zuwa ranar 20 ga wata Satumba 2021 domin ci gaba da shari'ar.

Matashiya

Onyebuchi Okafor wani dan kabilar Igbo ne mazauni garin Birnin kebbi wanda ya yi hulda da wata yarinya bafulatana kuma har ta sami juna biyu ta haihu.

Daga bisani rigima ya kaure tsakanin Onyebuchi da iyayen yarinyar saboda ya bukaci su bashi diyarshi. Bayan jayayya a gida, Onyebuchi ya kai kara a Kotun Majistare a jihar Kebbi. Yana neman Kotu ta mallaka masa yarinyar da budurwarsa ta haifa.

Sai dai mun samo cewa, Kotu ta tura lamarin ga hukumar Hisbah domin bincike kan lamarin. Hisbah ta gano cewa huldar da ya yi da budurwarsa haramtacce ne da ya kai ga aikata zina har yarinyar ta dauki cikin gaba da fatiha kuma ta haihu.

Sakamakon haka Hisbah ta bayar da shawara inda aka gurfanar da Okafo da budurwarsa a gaban Kotun Majistare bisa zargin aikata zina saboda baiyanar ciki da haihuwa. Bayan sauraron tuhuma da ake masu, Kotu ta tasa keyar Onyebuchi da budurwarsa zuwa gidan gyara hali kafin ranar zaman Kotu na gaba.

Bayan da aka dawo Kotu, an bayar da belin masoyan guda biyu. Sai dai bayar da belin Onyebuchi ke da wuya sai ya maka Atoni janar kuma Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi, Kwamishinan yansanda da hukumar Hisbah na jihar Kebbi a gaban Kotu.


Abin da ya kamata a lura

1. Onyebuchi Okafor kirista ne dan kabilar Igbo.

2. Yarinyar da ya yi wa ciki ba tare da aure ba yar kabilar Fulani ce kuma Musulma.

3. Idan yau Musulmi ne ya yi wa yar kabilar Igbo cikin shege tabbas ya shiga uku  duba da Sharia da ya gudana kwatankwacin irin wanan inda wata Kotu ta daure wani Musulmi Bakane hukuncin shekara 22 saboda ya Musuluntar da wata Yar kabilar Igbo ya aureta.

4. Alkalin da ke sauraron shari'ar Onyebuchi a babban Kotun tarayya na jihar Kebbi Musulmi  me.

5. Babu ruwan shari'ar da addini bisa amanar aikin Sharia.

6. Ba yarinya Karam ce Onyebuchi ya yi hulda da ya kai ga haihuwa da ita ba.

7. Da yardarta suka yi huldar lalata, mun samo cewa da kanta take samunsa  a shagonsa saboda soyayya.

Jan hankali

Bisa ga yadda lamurran ke tafiya kan tsarin sharia a gaban babban Kotun tarayya. Yana da kyau a kula da ire iren kalamai da cusa ra'ayi dangane da wannan batu a kafafen sada zumunta domin kauce wa yin katsalandan a harkar Sharia.

Kungiyar Lauyoyi Musulmi zata yi jawabi.

A lokacin zaman Kotu, mun kula da kasancewar  manyan Lauyoyi na kungiyar Lauyoyi Musulmi watau Muslim Lawyers Association MULAN redhen jihar Kebbi ke sauraron yadda shari'ar ke gudana kuma mun samo cewa za ta fitar da jawabi nan ba da dadewa ba.

Shawara

A saurari jawabin kungiyar Lauyoyi Musulmi na redhen jihar Kebbi MULAN.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN