Mutum tara aka kama da laifin karya dokar gudanar da aikin Hajji ta bana yayin da suka yi yunƙurin shiga wuraren da aka hana ba tare da shaidar amincewa ba.
Kamfanin labaran Saudiyya na SPA ya ruwaito wata sanarwa É—auke da sa hannun kakakin rundunar tsaro ta Masallacin Harami, Birgediya Sami Al-Shuwairekh, na bayyana hakan.
Sanarwar ta ce an ci tarar kowannensu riyal na Saudiyya 10,000 - kusan naira miliyan É—aya.
Birgediya Shuwairekh ya yi kira ga dukkan mahajjata da su yi biyayya ga dokokin na Hajjin bana, yana mai cewa "jami'an tsaro za su dakatar da duk wanda ya nufi Masallacin Harami da kewayensa (Mina, Muzdalifah, Arafat) ba tare da cikakkiyar shaida ba har zuwa ƙarshen watan Zul Hijja".
A yau Asabar 7 ga watan Zul Hijja na 1442 aka fara gudanar da aikin Hajjin, wanda za a kammala ranar 13 ga wata, wanda ya yi daidai da 13 ga watan Yuli.
Rahotun BBC