Dan Arewa ya kera mota mai amfani da wutan lantarki


Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa, Ya'u Mukhtar ya ce ya kera wannan mota mai amfani da wutar lantarki ne sakamakon irin wahalar da masu mota ke shiga wajen neman man mota.

"Abin da ya sa na fara tunanin kera wannan mota shi ne bisa la'akari da yadda masu mota ke fama a lokacin da kungoyi masu dakon mai ke yajin-aiki."

Ya ce yanzu haka dai ya kera motar ne domin hawan mutum biyu kuma zai lullube motar nan gaba kadan.

"Nan ba da jimawa ba za mu kera irin wannan motar mai daukar mutane da dama wato wadda ta fi wannan girma."

Ya'u Mukhtar ya yi amfani da kwanon keke mai kafa uku wajen kera wannan mota.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN