Yarsanda da ta kashe wani dansanda da dan kasuwa ta bindige kanta har Lahira a ban dakin gidan iyayenta


An sami gawar Yar sanda mai suna Caroline Kangogo wacce ake zargi da kisan wani abokin aikinta dansanda a garin Nakuru da kuma wani hamshakin dankasuwa a garin Juja. 

An Sami gawarta ne a gidan iyayenta a kauyen Anin da ke Gundumar Elgeyo Marakwet da karfe 8 na safe ranar Juma'a.

An kai gawarta dakin ajiye gawa da ke Gundumar Iten.

Wani babban dansanda ya ce,  an sami gawar Caroline ne q dakin wanka da raunin harbin bindiga a kanta.yarsanda ce hazika kuma mai basira ce wacce ke sashen bincike na yansanda. 

Sai dai ya ce mace ce mai tsananin fitina da zafin kai, wanda hakan yake bayyana tsakaninta da abokan aikinta wasu lokutta .

Lamari da ya sa shugabanninta a wajen aikin dansanda suka dauki matakin ladabtar da ita.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari