Duba cikakken rahotun irin rawa da jami'an tsaro mata ke takawa a harkar tsaron Najeria



Sojoji mata na cikin rundunonin tsaro na Najeriya da ke yaƙi da ƴan fashi a arewa maso yammaci da kuma mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

Mata Æ´an sa-kai sun bayar da gundumuwa da taka rawa ga magance wasu daga cikin matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

A watan Janairu ne aka baza sojoji mata 300 a hanyar Abuja zuwa Kaduna domin taimaka wa ayyukan tsaro musamman yaƙi da ƴan fashi masu satar mutane domin kuɗin fansa.

Ana ganin an tura mata fagen daga ne saboda yawan matsalolin tsaron da ke addabar kusan sassan Najeriya.

Masana na ganin jami'an tsaro mata suna tasiri sosai wajen magance matsalolin tsaro musamman rawar da suke taka wa wajen daƙile hare-haren ƙunar bakin wake da ake amfani da mata da kuma bayar da tsaro ga makarantu inda satar ɗalibai ta zama ruwan dare.

Sannan kuma masanan na ganin mata sun ƙware a wajen sasanta tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna.

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, abin da ya sa gwamnatin tarayya ke kira ga 'yan ƙasa baki ɗaya da su bayar da tasu gudunmawar a harkar tsaro.

Gwamnoni suna ganin akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta nemi taimako daga dakaru na ƙasashen waje ko kuma sojojin haya don yaƙar ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi.

Baya ga tashin hankali da ke faruwa sakamakon ayyukan masu neman ɓallewa daga ƙasar a yankin kudu maso gabas, akwai kuma hare-haren 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da faɗan ƙabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya a sauran yankuna.

Yayin da duk wannan ke faruwa, mata da yara ƙanana ne suka fi shiga halin ƙunci. To ko wace irin rawa matan ke takawa game da ayyukan kyautata tsaro a Najeriya?

Maganin masu garkuwa a hanyar Abuja-Kaduna

Sojojin Najeriya mata

ASALIN HOTON,KADUNA STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Sojoji mata 300 ne aka tura domin taimaka wa ayyukan tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

Ga duk wanda yake bin labaran da ke fitowa daga Najeriya ya san irin ƙaurin sunan da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi sakamakon kisa da kuma mutane don neman kuɗin fansa da ƴan bindiga ke yi kusan kullum.

Baya ga sauran matakai da hukumomi suka ce suna ɗauka, a ƙarshe sun yanke shawarar tura dakarun sojan ƙasar mata domin raba hanyar da ayyukan 'yan bindigar.

A ranar 28 ga watan Janairu ne kuma Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya tarɓi matan guda 300.

Gwamnan ya karɓi rukunin farko na sojoji mata daga rundunar musamman ta Nigerian Army Women Corps (NAWC) a sansaninsu da ke Kakau a kan babbar hanyar.

A Kaduna, 'yan fashi sun kashe mutum 937 sannan sun yi garkuwa da 1,972 a 2020 kaÉ—ai, kamar yadda wasu alÆ™aluman gwamnatin jihar suka bayyana.

Tsaron makarantu daga hare-haren 'yan fashi masu satar É—alibai

Mata 'yan Civil Defense a Najeriya

ASALIN HOTON,NSCDC

Bayanan hoto,

A baya jami'an tsaro na Civil Defense ba sa É—aukar bindiga, inda suka fi aikin bayar da tsaro a wuraren taruwar jama'a

Kafin yanzu, waÉ—anda aka fi yin garkuwa da su matafiya ne a yankin arewa maso yammacin Najeriya, waÉ—anda suka biya miliyoyin kuÉ—i domin su tsira.

Sai dai tun sace É—aliban makarantar Chibok 276 a 2014 da Boko Haram ta yi a Jihar Borno, 'Æ´an bindiga da dama sun bi sahu.

Tun daga 2014 zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoto, É—alibai kusan 2,000 ne aka yi garkuwa da su a makarantu a arewacin Najeriya.

Na baya-bayan nan shi ne wanda aka sace É—aliban sakandare ta FGC Birnin Yauri a Jihar Kebbi, inda har yanzu É—alibai da malamansu kusan 60 ke hannun masu garkuwa.

Mata 'yan Civil Defense a Najeriya

ASALIN HOTON,NSCDC

Bayanan hoto,

An É—aura wa mata 'yan Civil Defense alhakin kare makarantun sakandare daga sace É—alibai

Hukumar tsaro ta Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) ta tura dakarunta mata domin kare makarantu daga hare-haren 'yan fashin.

Kwamandan hukumar, Ahmed Audi, ya ce tura dakarun wani ɓangare ne na shirin tsare makarantu na Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida da kuma Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola, wanda ƴa umarci kwamandan da ya fito da tsari don kawo ƙarshen matsalar".

Kwamandan ya bayar da umarnin a ba su horo na wata ɗaya da kuma kayan aiki a dukkan jihohin ƙasar guda 36 tare da Abuja.

Akwai shiri da aka ƙaddamar na tabbatar da tsaron makarantu bayan sace ɗaliban Chibok a 2014 wanda aka kira "Safe School Initiative".

Shirin ya shafi kewaye makarantun domin tabbatar da tsaron É—alibai daga barazanar Boko Haram a arewa maso gabas.

Aƙalla dala miliyan 20 aka yi alƙawalin za a ware wa shirin na shekara uku wanda ya samu goyon bayan jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan ilimi, Gordon Brown, tsohon Firaministan Birtaniya.

An gina wasu makarantu na wuccin gadi ƙarƙashin shirin amma babu tabbaci ko an kewaye makarantun a yankin, sannan kuma shirin bai ƙunshi jihohin arewa maso yamma ba.

Daƙile harin ƙunar bakin wake

Wani bincike da cibiyar yaÆ™i da ta'addanci ta Combating Terrorism Center ta gudanar ya gano cewa, daga 2011 zuwa 2017, Boko Haram ta yi amfani da mata 'yan Æ™unar-bakin-wake aÆ™alla sau 244 a cikin hare-hare 338.

A 2018, 38 daga cikin yara 48 da ƙungiyar ta yi amfani da su wajen kai hari mata ne.

Rikicin na Boko Haram da ya fi Æ™amari a jihohin Borno da Yobe ya yi sanadiyyar kashe mutum kusan 350,000, a cewar rahoton Majalisar ÆŠinkin Duniya na baya-bayan nan.

Ba tare da wata rubutacciyar doka ba, sojojin Najeriya maza ba sa duba jikin mata wato caje su waɗanda ake zargi da aikata laifi, aƙalla dai ba a bainar jama'a ba.

Hakan ya sa mata 'yan ƙunar-bakin-wake kan kai hari ba tare da an gano su ba a asibitoci da makarantu da wuraren taruwar jama'a.

Mata da yara a Maiduguri na Jihar Borno

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Wasu mata da yaransu da Boko Haram ta kora daga garin Baga na Jihar Borno a 2013 bayan mayaƙan sun ƙona gidajensu

Wannan ya ƙarfafa gwiwar wasu mata a Jihar Borno shiga yaƙi da Boko Haram gaba-gaɗi, inda suka taimaka wajen gano mata masu yunƙurin kai hari da kuma kama su ta hanyar tattara bayanan sirri.

A ranar 9 ga watan Maris na 2018 ne Babban Hafsan Sojan Ƙasa na lokacin, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya kafa rundunar sojoji mata zalla mai suna Nigerian Army Women's Corps (NAWC).

Kafin naɗa Janar Buratai a muƙamin, shi ne kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta ƙasashen da ke yaƙi da Boko Haram mai suna Multinational Joint Task Force, (MNJTF). Babu mamaki a lokacin ne ya fahimci muhimmancin shigo da mata kai-tsaye cikin harkokin tsaro.

"Rundunar za ta sa a fahimci rawar da sojoji mata suke takawa wajen tsaron Najeriya," in ji Buratai a lokacin.

Tattara bayanan mutuwa

Gwamnatin Najeriya ba ta da wata ƙwaƙƙwarar hanya da take bi wajen sanin mutanen da ke rasuwa a kullum a ƙasar - walau ta hanyar rikici da tsaro ko kuma ta rashin lafiya.

Wannan dalilin ne ya sa wasu jajirtattun mata suka yunƙura domin tattaro sunayen irin waɗannan mutane a ƙarƙashin ƙungiyar #SecureOurLives.

Shirin wanda aka fara shi a watan Afrilun 2021, ya tattara sunan mutum 1,499 ya zuwa 22 ga watan Yuni.

Matan sun ce sun kafa yunƙurin ne domin samar da wata hanya tartibiya da za su dinga bin diddigin waɗanda rikice-rikice ke shafa.

Buky Williams na É—aya daga cikin jagororin shirin kuma ta faÉ—a wa Daily Trust cewa: "Duk sanda muka ji labarin an kashe wani sai mu ji cewa wani ne ya aikata amma muna mantawa cewa abubuwan suna faruwa ne ga wasu iyalai da abokai da 'yan uwa, kuma tattara sunayensu da muke yi girmamawa ce a gare su.

"Muna ganin da mun É—auki matakin da ya dace da ba su rasa rayukansu ba - Ba ma son irin waÉ—annan abubuwa su ci gaba, ba ma so mu ci gaba da rasa 'yan uwanmu. Ba wai babu maganin matsalar ba ne, kawai dai ba mu mayar da hankali kan waÉ—annan matsalolin ba ne."

Wata mamban ƙungiyar mai suna Ayisha Osori ta ce "abin mamaki ne a ce Najeriya ba ta da bayanai game da mutanen da rikici ya yi ajalinsu kwatakwata".

'Yin sulhu'

Masanin harkokin tsaro, Group Captain Sadiq Garba Shehu (mai ritaya) ya ce mata sun ƙware a wajen sasanta tsakanin ɓangarorin da ke rigima da juna.

"Wani ƙudiri na Majalisar Ɗinkin Duniya na 1235 ya bayyana cewa rawar da mata ke takawa a wuraren da aka yi yaƙi tana da muhimmanci sosai," in ji shi.

Captain Sadiq ya ce ganin cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi kaÉ—an, "tura mata wurare don bayar da tsaro zai bai wa mazan damar komawa wani wurin domin gudanar da ayyukan tsaron".

Aisha Wakil wadda aka fi sani da Mama Boko Haram, na cikin matan da aka sani waɗanda suka taka rawa wajen shiga tsakanin gwamnatin Najeriya da kuma ƙungiyar Boko Haram.

Cikin wata hira da kafar Channels TV a 2018, Aisha ta ce ita ce ta matsa wa mayaƙan Boko Haram domin su sako mata ɗaliban sakandaren garin Dapchi fiye da 100 da suka sace a watan Fabarairun 2018.

"Sun kira ni sun faÉ—a mani cewa su ne suka sace yaran nan. Na ce musu kun yarda na faÉ—a wa duniya cewa ku ne kuka sace su?, sai suka ce eh," a cewarta. "Ni kuma na faÉ—a wa duniya.

"Na ce musu ku dawo da yaran nan, kuma ina fata ba za su shafe kwana 1,000. Suka ce mani ba za su yi haka ba. Da na matsa musu sai suka ce kar na damu za su dawo da su."

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN