Kungiyar banga a garin Ukwulu, da ke karamar hukumar Dunukofia a jihar Anambra sun kama wani mutum mai shekara 34-mai suna KC Chukwuma aka `Ejima KC’ bisa zargin aikata sata a wani shago.
Chukwuma ya sato kwali biyu na indomie, sabulun wanka, barasa, madara da Milo daga shagon ranar Juma'a 23 ga watan Yuli.
Ya gaya wa yan bangan da suka kamashi lokacin da suke yi masa tambayoyi cewa shi ya taimaka wa kansa ne lokacin da ya gan shagon a bude. Sakamakon haka ya dauki abin da ransa ke so.Wani babban dan bangan ya gode wa al'umman garin bisa taimaka masu da bayanan gaggawa domin dakile miyagu daga ci gaba da addaban jama'ar garin.