Mutum 18 har da mutum 6 yan gida daya sun mutu a mumunan hatsarin mota


Mutum 18 har da mutum shida yan gida daya sun mutu a wani mumunan hatsarin mota da ya auku a karamar hukumar Doguwa a jihar Kano.

Hatsarin ya rutsa ne da wata mota kirar Volkswagen Sharon kuma ya auku ne a Gadar Shiburu Riruwai-Doguwa ranar Juma'a 23 ga wayan Yuli. 

Kwamandan rundunar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Kano Zubairu Mato, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon karyewar Gadar da ta hada Riruwai ds Doguwa sakamakon matsanancin ruwan sama.

Ya ce motar ta fada gadar ne ta tsunduma cikin ruwa tare da mutanen da ke cikin motar sakamakon haka duk wadanda ke cikin motar suka mutu har da mutum shida yan gida daya.. 

Wadanda suka mutu yan gida daya sun hada da  Malam Bashir Doguwa, Malami Gidan Tanimu Doguwu, Safiya Mukhtar Doguwu, Shashida Bashir me goro Doguwu, Fatima rabi u me goro Doguwu, Uzairu Bashir me goro Doguwu, dukkansu a karamar hukumar Doguwa a cikin jihar Kano.

Malam Bashir Doguwa da iyalinsa suna kan hanyarsu ne ta zuwa makarantarr Sakandare ta First Lady a karamar hukumar Dambatta saboda ya ziyarci diyarshi, Firdausi Bashir, wacce take cikin wadanda suke rubuta jarabawar NECO SSCE.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN