N10m da aka bamu sun yi kadan dole a bamu N30m kafin mu sako shi - Barayin da suka sace Ustazu


Wadanda suka sace Alhaji Abdulazeez Obajimoh, Daraktan AZECO pharmacy da ke garin Okene, a jihar Kogi sun ki su karbi kudin fansar Naira miliyan goma N10 da iyalinsa suka yi tayin su basu . Sun ce ala dole sai an basu Naira miliyan talatin N30 kafin su sako shi.

Wasu mutane ne dauke da bindigogi suka dauke Obajimoh a garin Iruvucheba da ke karamar hukumar Okenne a jihar Kogi ranar Lahadi, 11 ga watan Yuli.. 

Yanzu haka ana ci gaba da tuntuba tsakanin iyalinsa da yan bindigan da suka sace shi. Yayin da a daya bangare na hannun damansa sun yi kira ga Gwamnatin jihar Kogi ttare da jami'an tsaron jihar su fito da tsarin gaggawa domin kawo karshen kalubalen tsaro da yawaitar sace bayin Allah a fadin jihar.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN