Abin da ya faru da dilin da ya sa Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa mai Shari'a ta Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke Abuja, Binta Murtala Nyako, ta ɗage shari'ar jagoran masu rajin kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu zuwa ranar 21 ga watan Oktoba mai zuwa.

A ranar Litinin din nan ne aka so ci gaba da sauraron shari'ar Mr Kanu.

Sai dai rashin kai shi kotun daga bangaren jami'an tsaro ya sa an É—age shari'ar.

A ƙarshen watan jiya ne, Kotun Tarayya ta bayar da umarnin tsare jagoran 'yan a-waren, bayan masu gabatar da ƙara sun sake gurfanar da shi gabanta, bayan da aka kamo shi a ƙasar waje.

Gwamnatin Najeriya na tuhumarsa da laifuka 11, ciki har da cin amanar ƙasa da ta'addanci, da mallakar haramtattun makamai, da kuma kokarin tunzura jama'a don haifar da yamutsi.

Lauyoyin gwamnati da na jagoran 'yan a-waren sun hallara a kotun ko da yake wakilin BBC da ke kotun ya ce an hana wasu lauyoyi da ke wakiltar kungiyoyin kabilar Igbo shiga cikinta.

Wasu masu fafutuka a ƙasar sun yi gangamin goyon bayan Nnamdi Kanu a kofar babbar kotun.

Sai dai bayanai sun nuna cewa 'yan sanda sun kama masu zanga-zanga akalla bakwai.

Ran mai shari'a ya É“aci

A zaman kotun na ranar Litinin, mai shari'a Binta Murtala Nyako, ta bayyana bacin ranta bisa rashin gabatar da Mr Kanu.

Ta yi gargadin cewa ba za ta sake yarda da halin da aka nuna na kin gabatar da shi a gaban kotu ba.

Tun da farko, lauyan Mr Kanu Barrister Ifeanyi Ejiofor, ya yi korafin cewa hukumomin kasar sun ki barinsu su gana da mutumin da ake tuhuma.

Lauyoyi a kotun
Bayanan bidiyo,

Bidiyon yadda aka gurfanar da shugaban IPOB Nnamdi Kanu a kotu

A karshen watan Yuni ne ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, ya sanar da kama Mr Kanu, wanda ya tsere daga kasar.

Zuwa yanzu hukumomin Najeriya ba su bayyana kasar da aka kama jagoran 'yan a-waren na Biafra ba, sai dai kamfanin dillacin labarai na kasar ya ce wani karamin minista a ofishin harkokin wajen Birtaniya ya bukaci Najeriya ta yi musu bayani a kan hakan.

Shi dai Lauyan da ke kare Nnamdi Kanu ya ce an kama shi ne a Kenya, kuma an azabtar da shi tsawon kwana takwas kafin a mika shi ga hukumomin Najeriya.

Ofishin jakadancin Kenya a Najeriya ya musanta wannan zargi, sai dai kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra ta dage a kan haka.

Wasu shugabannin kabilar Igbo na cikin mutanen da suka halarci zaman kotun
Bayanan hoto, Wasu shugabannin kabilar Igbo na cikin mutanen da suka halarci zaman kotun
Short presentational grey line

Matashiya

Yayn ƙungiyar IPOB
Bayanan hoto, Yayan ƙungiyar IPOB

A watan Afrilun 2017 aka bayar da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya sai dai ya tsere daga kasar.

Sharudan belin su ne sai Mista Kanu ya gabatar da mutane uku wadanda za su tsaya masa kuma kowanne ya kasance yana da naira miliyan 100.

A watan Maris na 2019 ne wata kotun tarayya ta soke belin da ta bai wa Mr Kanu saboda zargin tsallake belin sannan ta umarci hukumomin tsaro na ciki da wajen Najeriya su kamo mata shi.

Daga bisani ne jami'an tsaron Najeriya suka ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN