Yadda mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammad ya mutu


Shafin BBC Hausa ta ruwaito cewa, mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.

Ya mutu yana da shekarun 84 bayn ya sha fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka shaida wa jaridar Berlingske a ranar Lahadi.

Westergaard mai zanen barkwanci ne a jaridar nan mai ra'ayin ƴan mazan jiya ta Jyllands-Posten a farkon shekarun 1980.

Ya yi suna ne a shekarar 2005 bayan wani zanen ɓatanci na Annabi Muhammad a jaridar.

An wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutikar da Musulmi masu raji suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama na Musulmai.

Shi ne ya yi zane-zanen barkwanci 12 masu cike da ce-ce-ku-ce da jaridar ta wallafa, da suke sukar Musulunci.

Zanen da ya ɗaga hankalin al'ummar Musulman duniya shi ne wanda ya nuna wani da ya danganta shi da Annabi Muhammadu yana sanye da rawani mai alamar bam.

Nuna duk wani hoto ko zane da ake alaƙanta shi da Annabi Muhammadu haramun ne a Musulunci, kuma Musulmai da dama suna ɗaukar irin waɗannan zane-zane a matsayin cin mutuncin addininsu da gangan.

Zanen barkwancin ya jawo zanga-zanga a Denmark da sauran ƙasashen Musulmai.

An kai hare-hare ofisoshin jakadancin Denmark, kuma gwamman mutane sun mutu a zanga-zangar da suka biyo baya.

Wallafa zanen barkwancin ya bar baya da ƙura sosai. A shekarar 2015, mutum 12 aka kashe

Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.

A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya karasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar 'yan sanda.

A shekarar 2008, hukumomin Denmark sun tuhumi mutum uku da shirya kisan Westergaard.

Shekara biyu bayan nan sun kama wani mutum da wuƙa da ya shiga gidansa.

Daga baya aka kama Mohamed Geele da laifin ƙoƙarin kisan kai da ta'addanci aka kuma ɗaure shi har tsawon shekara tara.

A shekarun ƙarshe na rayuwarsa, dole Westergaard ya dinga zama da masu tsaron lafiyarsa a wani ɓoyayyen waje.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters a 2008, Westergaard ya ce ba ya da na sanin zanen ɓatancin da ya yi.

Ya ce zanen ya jawo "muhawara mai muhimmanci" kan matsayin Musulunci a ƙasashen yamma.

"Zan sake yin abin da na yi saboda ina ganin wannan rikicin zanen barkwancin hanya ce ta ƙarfafa yadda za a rage rungumar aƙidun Musulunci," ya ce.

"Muna tattauna batun al'adun biyu, da addinan biyu yadda ba a taɓa yi ba a baya, kuma hakan yana da muhimmanci," a cewarsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN