Yi wadannan ababe guda 2 domin kaucewa yin gudawa sakamakon cin naman Ragon Layya


Wasu mutane sukan yi fama da lalacewar ciki da har da gudanawa sakamakon cin naman Ragon Layya.

Sai dai akwai wasu hade-hade na gida bayan cin dabino da ke taimakawa wajen hana lalacewar ciki sakamakon cin naman Ragon Layya.

Domin kariya ga lalacewar ciki ko gudanawa sakamakon cin naman Ragon Layya. 

1. A samo tsamiya a jika, bayan ya jiku sai a dama. A sami ludayi daya a sha.

2. A samo Lipton sai a samo lemun tsami a matsa a cikin sai a sha da dan duminsa.

Da yardar Allah, yin haka zai kare ka daga gudanawa sakamakon cin naman Ragon Layya. 
Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari