Birnin kebbi: Yadda aka ajiye wani Jariri cikin dare a kofar gidan Kwamandan Hisbah a Unguwar Badariya aka gudu aka barshi


An kawo wani Jariri da aka lullube da farin kyalle aka ajiye a daidai kofar gidan Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kebbi a Unguwar Badariya da ke garin Birnin kebbi da dare ranar Alhamis 15 ga watan Yuli.

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa wasu, ko wani ne da ba a san ko waye ba suka kawo jaririn suka ajiye shi da misalin karfe 8:15 na dare lokacin da Kwamandan Hisbah yake Masallaci domin gudanar da Sallar Isha'i. 

Yanzu haka babu wanda ya fito ya yi ikirarin mallakan wannan Jariri. Sai dai jaririn na hannun wata mata a hukumar Hisbah, kuma yana cikin koshin lafiya bayan Hisbah ta kai shi Asibiti inda gwajin Asibiti ya tabbatar yana lafiya kalau kamar yadda majiyarmu ta samo.

Wa zai kula da jaririn har ya girma 

Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa akwai yiwuwar hukumar Hisbah ta kai jaririn gidan Marayu da ke karkashin ma'aikatar kula da harkokin mata na jihar Kebbi, watau Kebbi state ministry for women affairs and social welfare domin ci gaba da samun kulawa. 

Abubakar Muhammed Augie Daraktan sharia


Ko shiryayyen lamari ne ?

Bisa ga dukkan alamu, duk wanda ya kawo wannan Jariri ya ajiye a kofar gidan Kwamandan Hisbah ya yi ne da manufar ganin cewa Hisbah ta dauki dawainiyar jaririn da ake zargin an same shi ne da hanyar huldar gaba da Sadaki ballle daurin Aure kuma ya zama 'da na gaba da Fatiha.

Allah ya kiyaye ba abin da ya sami Jariri kafin ya sami agaji.

Babu tabbacin hakikanin lokacin da aka ajiye Jariri kafin fitowar Kwamanda daga Masallaci bayan Sallar Isha'i. Allah ya kiyaye Karnuka basu yi wa kowane bangare na jikinsa lahani ba kafin isowar jama'a.

Suleiman Muhammad Kwamandan Hisbah jihar Kebbi

Hukumar Hisbah ta yi kira ga mai Jariri cewa ya ji tsoron Allah ya zo ya karbi jaririnsa.

Kwamandan Hisbah na jihar Kebbi ya yi kira ga wanda ke da alhakin mallakar wannan Jariri, cewa ya ji tsoron Allah ya zo ya karbi jaririnsa. Domin yadda aka lullube wannan Jariri da farin kyalle haka wata rana za a lullube shi ko ita da farin kyalle a kai Makabarta a bizine a Kabari. 

Kuma Allah zai tayar da shi ranar kiyama domin yin hisabi da mahaifiyarsa da ga jefar da shi ba tare da ya yi mata laifin komi ba.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN