Duba abin da hafsan dansanda ya aikata a kan titi a bainar jama'a bayan ya hadiye kwaya


Rundunar 'yan sandan JIhar Abia ta tsare wani ɗan sanda mai muƙamin mataimakin sufuritanda bayan ya zaro bindiga tare da yin harbe-harbe a sama. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Ifeanyi Henry ya fito da bindiga tare da hawa kan titi yana cin zarafin mata da ƙananan yara da 'yan kasuwar yankin Okwu na Uka da ke birnin Aba da ke kusa da ofishinsu, a cewar rahoton Daily Trust.

Rahoton ya ce jami'in ya fara aikata hakan ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Asabar.

Wasu da Daily Trust ta zanta da su a wurin sun bayyana cewa ɗan sandan ya lalata kayan wata mata mai sayar da kayayyaki a kusa da ofishin sannan ya lakaɗa mata duka. Shaidun sun yi zargin cewa da alama a bige yake sakamakon ƙwaya da ya sha.

"Ina yin tur da abin da ɗan sandan ya aikata kuma ina tabbatar muku cewa yana tsare yanzu haka da zummar hukunta shi," in ji SP Geoffrey Ogbonna, kakakin 'yan sandan Abia.

"Rundunar 'yan sandan Najeriya mai ɗa'a ce. Haka nan akwai ƙa'idojin aiki da suka tanadi hukunta duk wani jami'i komai girman muƙaminsa."

Sai dai ba a bayyana ko ɗan sandan ya harbi wani ba, yayin da aka kai waɗanda ya jikkata asibiti.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN