Labari mai zafi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace mata


Yan bindiga sun kashe wani mutumin kauye tare da yin garkuwa da mutane 7, ciki har da mata uku a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a kauyen Anguwar Gajere dake karkashin yankin Kutemashi na karamar hukumar, a ranar Asabar 17 ga watan Yuli.

An kuma gano cewa 'yan bindigan sun sace shanu sama da 50 daga kauyen.

Labari mai zafi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace mata

'Yan bindiga | Hoto: dailytrust.com.ng

Wani mazaunin yankin, Mohammed Birnin Gwari, ya shaida wa Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa ’yan bindigan sun zo ne a kan babura da misalin karfe 1 na rana.

Mohammadu ya ce:

"'Yan bindigan sun sace mata uku, maza hudu da shanu da dama bayan sun kashe mutum daya,"

Wani tsohon Kansilan yankin, Adamu Kutemashi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai, rundunar ‘yan sanda ta jihar ba ta ce komai a kan lamarin ba kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Jalige Mohammed, ya yi alkawarin ba da bayanai daga baya.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN