Kebbi: NSCDC ta kama wanda ya yi wa yar shekara 5 fyade da wanda ya yi yunkurin sace yar shekara 3 a Badariya


Rundunar tsaro ta  farin kaya Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) reshen jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekara 35 bayan ya yi wa yarinya yar shekara biyar fyade,

Yayin tattaunawa da manema labarai a Birnin kebbi, Kwamandan rundunar na jihar Kebbi Umar Musa-Bala, ya ce wanda  aka kama ya tsere bayan ya aikata laifin Amma an kama shi ranar 6 ga watan Yuli.

Ya ce wanda aka kama ya aikata laifin ne a Unguwar shiyar fara a garin Jega da ke karamar hukumar Jega a jihar Kebbi ranar 13 ga watan Yuni, amma ya tsere. Sai dai jami'an rundunar sun sake kama shi ranar 7 ga watan Yuli suka zo da shi Birnin kebbi.

Kazalika, Kakakin rundunar ta jihar Kebbi, ya ce rundunar ta kama wani mutum dan shekara 22 mai suna Hussaini Abubakar Dan asalin Unguwar kofar Masama a garin Gwandu na karamar hukumar Gwandu. An kama shi ne bayan ya dauke wata karamar yarinya mai shekara 3 a Unguwar Badariya a garin Birnin kebbi, amma kafin ya tafi da yarinyar, makwabta sun ankara kuma suka sanar da jami'an hukumar wanda suka je suka kama shi.

Ya ce sun gano lokacin bincike cewa, Hussaini yana son ya tafi da yarinyar ne zuwa wani waje daban bisa wata manufa..

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN