Yan bindigan sun sace Manajan Sokoto Rima River Basin Development Authority (SRRBDA), na yankin Dutsin-Ma, Labaran Muhammed Dandume cikin daren ranar Alhamis, OBSERVERS TIMES ta ruwaito.
Wata majiya a Dutsin-Ma ta ce mutanen sun dauke Manajan ne a gidansa da ke gidajen SRRBDA da misalin karfe 11:47 na dare ranar Alhamis.
Duk da yake an sami mabanbantan bayanai kan Labarin yadda Yan bindigan suka sace Manajan a samame da Yan bindigan suka gudanar a kasa da minti 20.
Kakakin hukumar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce Yana sane da faruwar lamarin. Sai dai ya ce a bashi lokaci domin tattara bayanai kafin ya yi bayani kan lamarin.