Birnin kebbi: Jami'in NSCDC ya mutu da damarar aiki sakamakon hatsari da babban mota


Wani jami'in rundunar Nigerian Security and Civil Defense Corps NSCDC mai suna Amos Manga ya mutu sakamakon wani hatsarin mota a garin Birnin kebbi ranar Juma'a 2 ga watan Yuli.

Wani ganau ya shaida wa shafin labarai na ISYAKU.COM cewa Lamarin ya faru ne da yamma daidai mahadar hanya da ke kan tagwayen hanya na Sani Abacha kusa da hanyar shiga kauyen Kanikawa lokacin da marigayin sanye da damarar tufafin Kaki na aiki, ya yi kokarin juyawa yayin da ya ketaro daga mahadar titi amma sai tsautsayi ya sa ya fadi da babur da yake tukawa sai wata babbar motar da ke tafe ta bi ta gefen jikinsa.

Kazalika mun samo cewa marigayin dan asalin garin Manga ne a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Mun kuma samo cewa samun Labarin mutuwarsa ke da wuya, sashen aje gawa na Asibitin Sir Yahaya ya cika da jama'ar kasar Zuru da wasu jami'an rundunar NSCDC domin nuna tausayawa.

Marigayin ya bar mata da yaya.

Tuni Mawallafin shafin ISYAKU.COM ya isar da taaziyarsa ga kanin marigayin amadadin dukkannin ma'aikatan shafin ISYAKU.COM.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari