Duba abin da kasar Kenya ta ce dangane da kama Nnamdi Kanu


Shugaban hukumar shige da fice na kasar Kenya, Alexander Muteshi, ya musanta cewa ya san da batun kama Nnamdi Kanu shugaban IPOB da kuma dawo da shi Nigeria, Daily Trust ta ruwaito.

An kama Kanu ne a karshen makon da ta gabata sannan aka taso keyarsa a jirgin sama zuwa Abuja a ranar Lahadi.

An gurfanar da shi gaban Mai shari'a Binta Nyako na babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata inda ta umurci hukumar tsaron farin kaya DSS ta ajiye shi har zuwa ranar 26 ga watan Yulin 2021.

Gwamnatin tarayyar Nigeria ba ta ce komai ba game da inda aka kama Nnamdi Kanu.

Sai dai cikin wata sanarwa da Kingsley Kalu, kanin shugaban na IPOB ya fitar a ranar Laraba ya yi ikirarin a Kenya aka kama Kanu kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya ce:

"A yayin da ya kai ziyara Kenya, an kama Kanu aka tsare shi sannan aka mika shi da hukumomin Nigeria suka dawo da shi Nigeria."

"Gwamnatocin Nigeria da Kenya sun keta hakkin dan uwana. Sun saba doka. Kama mutum a mika shi ga wata kasa babban laifi ne."

Abin da gwamnatin Kenya ta ce game da kama Nnamdi Kanu


Amma yayin hirar da ya yi da The Nation, wata jarida a Kenya a ranar Alhamis, Muteshi ya ce bai da tabbas cewa a Kenya aka kama Kanu.

Amsar da Muteshi ya bawa Nation game da kama Kanu:

"Ba zan iya sani ba."

"Ban san ya shigo kasar nan ba. Zan iya sani idan wani ya shigo kasar ne kawai ta hallastaciyar hanya."

Ba a sani ko Kanu ya shiga Kenya ba bisa ka'ida ba.

Ana tuhumar shugaban na IPOB ne da laifin cin amanar kasa kafin ya tsere bayan an bashi beli.

Kanu ya cigaba da ingiza magoya bayansa ta hanyar kafafen watsa labarai kamar Radio Biafra da dandalin sada zumunta.

Ya kuma kafa wata kungiyar tsaro mai suna ESN da ake zargin tana kai wa hukumomin gwamnati da mutane hari

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN