Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS


Wasu yan bindiga kimanin 20 sun kutsa Alaafia Estate a Orogun, Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun raba mutane da kayayyakinsu da kudadensu, The Punch ta ruwaito.

The Nation ta ruwaito cewa wasu daga cikin yan bindigan sun yi amfani da na'urar tura kudade na POS wurin sace kudade daga hannun wadanda ba su da tsabar kudi a hannunsu.

An ce sun tafi da katin ATM din wasu daga cikin mutanen tare da lambar sirri ta PIN dinsu domin su cire kudaden a yayin da suka fuskanci matsala ta sabis.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ce kimanin gidaje 25 yan bindigan suka shiga suka yi wa fashin.

Yan bindigan, cikin fushi sun lalata kayayaki da dama a gida na 25, inda suka zargi wasu daga cikin yan gidan da lekensu suna kallon yadda suke fashin wasu gidajen.

An ruwaito cewa daga bisani an sanar da jami'an yan sanda abin da ke faruwa kuma da isowarsu yan bindigan sun cika wandunansu da iska sun tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Mr Adewale Osifeso, ya ce an sanar da yan sandan misalin karfe 3 na dare kuma sun tura wasu jami'ansu wurin.

Ya ce, "Da ganin yan sanda, yan bindigan suka tsere bayan gumurzu da suka yi. A yayin hakan, an kwato bindiga pistol da adduna uku da jaka dauke da tufafi da layukan waya masu yawa."

Ya ce ana cigaba da bibiyan sahun yan bindigan domin a kamo su.

A wani labari daban, Gwamnatin jihar Kano ta hana shan sigari a bainar jama'a domin yaki da annobar cigari a yayin da ake samun kimanin mutane 16,100 da ke mutuwa duk shekara daga matsaloli masu alaka da cigari, Daily Trust ta ruwaito.

A wani mataki na habbaka lafiya da rayuwar al'umma a jihar na Kano, gwamnatin jihar ta ce ta ware kudade da dama domin yaki da cututtuka marasa saurin yaduwa kamar hawan jini, sikila, asma da ciwon huhu masu alaka da shan cigari da sauransu.

Source: Legit.ng

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN